Sunday, November 4, 2012

KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA 1.HASSADA:Hakika Hassada yana daya daga cikin abinda yake cutar da al'umma.Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) Yace"Kashedin ku da hassada domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye Audiga". 2.ANNAMIMANCI:Annamimanci shima yana cutar da al'umma. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace "Lokacin da aka yi mi'iraji dani mun wuce wasu mutane masu zara zaran kumbuna,suna jan naman fuskokinsu,da jikkunan su,sai nace su wanene wainnan Ya Jibrilu,sai yace sune wainda suke cin naman mutane".Don haka akwai tanadin azaba mai tsanani ga masu cin naman mutane. 3.GIRMAN KAI:Kowa da irin nashi nau'in girman kan,akwai girman kai na rashin karban gaskiya, akwai kuma girman kai na wulakanta Jama'a.Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace"Mai girman kai koda kwayen zarrane ba zai shiga Aljannah ba". 4.GIBA:An tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) menene Giba,yace ka ambata ma dan'uwan ka abinda baya so. 5.KARYA:Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yana cewa"Yana daga cikin manyan laifuka ka bawa dan'uwan ka labari,shi yana dauka gaskiyane amma kuma kai karya kakeyi,wannan shima yana cutar da al'umma,domin karya tana leading mutum zuwa ga Abubuwa masu yawa,kada kaji tsoro ko faduwar gaba indai abinda kake fada gaskiyane,koda dukkan mutane zasu ki yarda dakai. 6.KADE KADE DA RAYE RAYE: Tabbasa yawan jin waka yana kashe zuciyar bil Adama yana lalata zuciya,yana kuma haifar da sharri,yana kuma samar da mummunar dabi'a.Wani sai yayi sati bai karanta Qur'ani ba,kuma baya saurara,wani ma gani yake kauyancine saka karatun Qur'ani a cikin wayar sa,domin su zigi zasu ce bai waye ba.zaka sami mutum yana da Memory Card mai nauyi, amma ba abinda yake ciki sai wakoki da videos masu nauyi, hakika dan'uwa ka dauko hanyar halaka. 7.ZINA:Zina shima yana cikin munanan halayen da suke cutar da al'umma. 8.KALLON FINA FINAN BATSA:HMM, wannan musifa ya riga ya yadu a duniya,laifine babba ma'aurata su fadi sirrin su,sai gashi yau ana samun mutanen da suka mai da shi sana'a,wai kuma musulmi ya cire kudin shi yaje ya siya,hakika duk mai kallon wannan fina finan yayi asara babba wallahi,idan kana kallo ne domin ka ragyewa kanka sha'awa to wannan hudubar shaidan ne,babu wani ragye maka sha'awa da zayyi,sai dai ma kullun ya sa muku kwadayi.Ba anan shegantakar ta tsaya ba hatta mijin aure musamman sabon aure,haka zaije ya siyo musu wai saboda su koyi yadda akeyi,wannan abin yana faruwa sosai a cikin al'umma. Gaskiya sai munyi da gaske sannan mu yaki shaitan. 9.CIN HARAM:A gaskiya yawancin mutane na wannan zamanin suna cin haram idan kana cin haram ko addu'a kayi ba za'a amsa maka ba. Yanzu akwai wani abin tsiya da Attajirai suke yi,idan suka ci haram suka wawuri kudin talakawa,suka yi handama da babakere,sai kuma su yawaita aikin lada,su rinka daukan kudin haram suna gina masallaci da islamiyya,da zuwa aikin hajji da sadaqa,su a jahilcin su wai wannan aikin ladan shi zai kankare musu zunuban su,shi zai hana Allah yayi musu azaba,Wai kaji sune zasu yi ma Allah wayau, sun mata Manzon Allah yace"Lallai Allah Madaukakin sarki mai tsarki ne,kuma baya karban aiki sai mai tsarki".Kudin da kaci basu da tsarki,so tayaya Allah zai amsa maka Ibadun da kayi da wannan kudin.ka cuci 'ya'yan ka raine su da dukiyar haram hakika Allah zai muku hisabi. 10.CIN AMANA:Amana muka rasa yanzu mu musulmai,daidai kun mutane ne masu Amana,yanzu kafin ka sami wanda zai rike maka amanar dukiyar ko iyalinka sai ka bincika, shiyasa yanzu kafirai basa jin tsoron mu,shiyasa suke tattakamu,suke karkashe mu,suke wulakanta mu suke cin mana mutunci.Don haka cin amana yana daya daga cikin MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'AUMMA. Allah Ya sa mu cika da imani!


No comments:

Post a Comment